Raisi Iran Zata Bude Cibiyar Kasuwancinta A Kasar Qatar.
Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Raisi ya bada sanarwan cewa za’a bude cibiyar kasuwanci ta kasar Iran a birnin Doho na kasar Qatar nan ba da dadewaba.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a jiya talata da yamma bayan ya kammala ziyarar kwanaki biyu zuwa kasar ta Katar. Shugaban ya kara da cewa ministocin masana’antu na kasashen biyu zasu fara aiki tare don kauda duk wani shingen da zai iya hana harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu tafiya.
Shugaba ya ce manya-manyan ‘yan kasuwa na kasar Katar a shirye suke su fara harkokin kasuwanci da kasar Iran. A ziyarar kwanaki biyu da ya kai kasar Katar, kasashen biyu sun rattaba hannu a kan yarjeniyoyin kasuwan har guda 14, sannan Iran da kasar Venezuela sun cimma matsaya kan al-amuran makamashi a gefen taron kasashen masu arzikin iskar gas a duniya da aka gudanar a jiyaq Talata.