Raisi; Iran Babbar Amintacciyar Abokiyar Tarayyar Nahiyar Africa Ce.
Da yake isar da sakon taya murnar zayowar ranar Africa ga takwaransa na kasar Senigal Macky Sall da sauran Alummar Africa shugaban kasar Iran Ibrahim raisi ya fadi cewa Iran itace babbar Amintacciyar abokiya ga nahiyar Africa.
Da yake ishara game da rawar da kungiyar tarayyar Africa ta ke takawa wajen tunkarar manufofin nuna wariya da mulkin malaka y ace jamhuriayr Musulunci ta iran ita ce Amintacciyar abokiyar dogaro ga dukkan Alummar Africa
A game da batun karfin da iran take da shi a bangaren injiniya yace Tehran da Dakar suna da kyakkyawan dangantaka tsakaninsu , sai dai har yanzu ba’a kai matakin da ake so ba, akwai bukatar bunkasata ta kai babban mataki a kowanne bangare.
READ MORE : Don shayar da yahudawan sahyoniyawan wuta su danne maruwaitan gaskiya.
Ana sa bangaren shugaban kasar Senigla Macky Sall ya godewa shugaban kasar iran game da sakon taya murnar tanar Africa da ya aike das hi,kuma ya nuna irin kulawa ta musamman da iran take nunwa Nahiyar Africa, kuma ya nuna irin kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasarsa da sauran kamfanonin kasar iran, yace ya zo kasar iran sau 2 ya ga irin ci gaban da ta samu.