Ra’isi; Dawo Da Alaka Tsakanin Iran Da Saudiyya, Na Da Mahimmanci Ga Tsaron Yankin.
Shugaba Ibrahim Ra’isi Na Iran, ya ce dawo da alaka tsakanin kasarsa da Saudiyya zai amfani sha’anin tsaro a yankin.
Sayyid Ra’isi ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da ministan harkokin wajen Iraqi Fuad Hussein da ke ziyara a birnin Tehran ranar Litinin.
Shugaban kasar ta Iran ya yaba da rawar da Iraqi ke takawa a ci gaban yankin, yana mai cewa, ” atakan da Iraqin ta dauka na inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin ba tare da sanya baki na kasashen waje ba, yana taimakawa gayen wajen kara karfafa alaka a yankin’’
A daya bangaren kuma da ya tabo halin dambarwar da aka shiga a Iraqi, shugaban kasar ta Iran, yma dukkanin bangarorin siyasa na kasar bisa tanadin tsarin mulki.
A nasa bangaren, ministan harkokin wajen Iraqin, Fujaddada cewa tabbatar da tsaro da zaman lafiya a kasar zai kasance ne kawai ta hanyar tattaunawa tsakanin ad Hussein, ya yaba da irin goyon bayan da Iran ke ba wa kasarsa wajen samar da zaman lafiya da tsaro ba tare da katsewa ba, yana mai cewa kasarsa za ta ci gaba da kokarin kyautata alakar Iran da Saudiyya.