Ra’isi; Ba Wata Kasa A Duniya Wacce Zata Tursasawa Iran Yi Ko Barin Wani Abu.
Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana cewa babu wata kasa a duniya wacce zata iya tursasawa mutanen kasar Iran yi ko barin wani abu.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Alhamis da dare, a lokacinda yake amsa tambayoyin ‘yan jarida bayan ya kammala ziyara da ya kai lardin Chahar-Mahal Bakhtiyar.
Shugaban ya kara da cewa kudurin da hukumar IAEA ta samar don takaita shirin nukliyar kasar Iran ba zai hana kasar ci gab aba, kuma ba zai hanata neman hakkinta na amfani da fasahar nukliya ta zaman lafiya ba.
Ra’isi ya kara jaddada cewa gwamnatin kasar AMurka ta tabbatar da cewa shirin takurawa mafi muni wanda tayiwa kasar Iran bai yi tasiri wajen hana kasar ci gab aba. Kuma da sannu a hankali tasirin da yayi a bangaren rayuwar mutanen zai tafi shima.
A ranar laraba da ta gabata ce, majalisar gwamnoni na hukumar IAEA ta amince da wani kuduri wanda kasashen Amurka, da wasu kasashen turai 3 suka gabata wanda ya nuna cewa Iran bata bada hadin kai da ya dace da hukumar ta IAEA.
Tuni dai gwamnatin kasar Iran ta fara maida martani tare da kashe na’urorin daukar hoto masu yawa na hukumar da suke aika hotunan ayyukan nukliya a cibiyoyin nukliyar kasar ga hukumar.