Wani rahoton bincike na baya bayan nan da mujallar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato “The Lancet” ya nuna cewa, a cikin shekaru 40, adadin mutanen da suka mutu a sanadiyyar cin zarafi da jami’an ‘yan sandan kasar Amurka suka yi musu, an kwashe sama da kaso hamsin bisa dari na adadin idan an kwatanta da hakikanin alkaluman.
Marubucin wannan nazari ya bayar da rahoton cewa, bayanan bogi ko kuma rashin kididdige wadannan mace-macen da aka samu zai kara boye girman mummunar matsalar nuna wariyar da hukumomin tabbatar da tsaron Amurka ke aikatawa.
Dama dai a kwai alamun shakku game da rahoton da hukumomin suka fitar fitar dangane da cin zarafin fararen hula da ‘yan sanda keyi a amurkan, wanda mafi yawanci hakan ke sabbaba rasa rayukan wadanda abin ke shafa.
‘Yan sanda a kasar da amurka sun shahara da cin zarafin fararen hula, abnda ake zargin ana basu horo ne danhane da hakan kuma ana dora su kan wannan mummunar turba ta cuzgunawa mutane.
Gwamnatin amurka dai nata kokarin boye wadannan munanan ta’asa da ‘yan sandan keyi amma rahohon lanchet ya tona mata asiri tare da bankado abinda take kokarin boyewa duniya.