Cibiyar da ke da kula da abinci ta nahiyar Afrika ta ta bada rahoto cewa, matsalar karancin abinci na ci gaba da girmama a yankin Sahel, da kasashen yankin yammacin Afrika, inda yanzu haka kimanin mutane miliyan 23 da dubu 700 kwatankwacin kashi 7.4 na al’ummar kasashe 15 da aka nazarta ke cikin matsalar.
Rahoto ya nuna cewa wannan adadi dai na iya karuwa a wannan lokaci na tsakanin rani da damina kamar yadda alkaluman cibiyar suka nuna cikin wani rahoton karshen shekara da ta fitar.
Rahoto ya nuna cewa kimanin mutane miliyan 33 da dubu dari 4 ne za su iya fadawa cikin matsananciyar barazanar karancin abinci idan har ba a dauki wasu matakai na gaggawa ba, a cewar wata kwararriya daga cibiyar wadda ke taronta ta hoton bidiyo.
Jami’ar ta ce adadin na wakiltar kashi 10.5 na al’ummomin kasashen.
Laurent Bossard babban daraktan cibiyar hadakar kasashen sahel da na yammacin afrika (CSAO), ya ce babban dalilin faruwar matsalar karancin abincin ita ce, rashin tsaro da tashe tashen hankulla da yankin ke fama da shi
Inda ake da fagagen daga guda 2 daya na cikin yankin da ya hada iyakokin 3 da suka hada kasshen Mali, Burkina Faso da Niger, inda ake kai munanna hare haren ta’addanci dake haifar da hasarar rayuka masu yawa daga mayakan kungiyoyin yan ta’addan Al-Qaïda (ISIS).
Fagen daga na biyu kuma shi ne wanda ya hada yankunan kasashen yankin tafkin Tchadi Najeriya Nijer Tchadi da kuma Kamaru, yankin da ya kasance maboyar kungiyar Boko Haram da ballalinta, da kuma kumgiyar Iswap dake biyayya ga kungiyar ISIS.