Rahotannin game da yaƙi a Ukraine zuwa yanzu…
Yayin da muke fara kawo rahotannin a wannan safiya, ga abubuwan da ke faruwa a taƙaice:
- Ana ci gaba da ruguntsumi a tsakiyar birnin Mariupol, wanda Rasha ke yi wa luguden wuta. Gwamnatin Ukraine ta ce fararen hula kusan 100,000 ne yaƙin ya tarfa ba tare da abinci da ruwa ko abin ɗumama ɗaki ba
- Sai dai Shugaban Ukraine ɗin Volodymyr Zelensky ya ce duk da fafatawar da ake yi an yi nasarar kwashe mutum 7,026 daga Mariupol ranar Talata
- Rundunar sojan Ukraine ta yi iƙirarin cewa “gwiwar dakarun Rasha ta yi sanyi”, kuma yanzu mahukunta a Rashar na yunƙurin ɗaukar tsofaffin sojoji don shiga yaƙin
- Mai magana da yawun shugaban Rasha, Dmitry Peskov, ya ƙi ya kawar da yiwuwar amfani da makamai masu guba. Cikin wata hira da kafar yaɗa labarai ta CNN, Mista Peskov ya ce za a iya amfani da su idan aka yi wa ƙasarsa barazana
READ MORRE : Ministan Yamen; Akwai abubuwan mamaki kan hanyar da za su canza ma’auni na iko.
- Amurka ta yi Allah-wadai da batun, tana mai cewa na “rashin kamun kai ne kuma ba haka ƙasar da ke da makamin nukiliya ya kamata ta yi ba”
- Kazalika, Amurka ta ce dakarun Ukraine na samun nasarar sake ƙwace iko da wasu garuruwa daga hannun na Rasha, musamman a yankin kudancin ƙasar