Shafin Sharq al-ausat ya bayar da rahotanni cewa, jami’an tsaron Lebanon sun samu nasarar cafke daya daga cikin wadanda suka kai wa janazar wani dan Hizbullah hari a jiya.
Bangaren ayyukan asiri na soji a kasar Lebanon ya bada rahotanni cewa, an samu nasarar kame daya daga cikin mutanen ad suka kai harin ne a lokacin da ake janazar daya daga cikin dakarun Hizbullah da wasu suka kashe shi a ranar Asabar da ta gabata.
Bayanin jami’an tsaron ya ce waanda suka yi hakan za su fuskanci shari’a domin fuskantar hukuncin abin da suka aikata, musamman ma ganin cewa a lokacin janazar sun kuma sake kashe wasu mutane uku.
Kungiyar Hizbullah ta ce ba za ta yi komai kan hakan ba, amma dole ne a kan jami’an tsaro su kama duk wanda yake da hannu cikin lamarin kuma ya fuskanci shari’a.
Tuni dai shugaabannin kasar ta labanan sukayi Allah wadarai da wannan harin inda suka zargi kasashen ketare musamman haramtacciyar kasar isra’ila da kitsa wannan aikin ta’addanci.
Shugabannin na labanan sun tabbatar da cewa suna tare da kungiyar ta hisbullah kuma zasu bata kowanne irin goyon baya domin lalubowa tare da kamo masu hannu a harin domin girbar abinda suka shuka.
A wani labari na daban isra’ila ta fara nuna damuwa game da bangado leken asirin da ake zargin kamfanin NSO na kasar da hannu a ciki.
A halin da ake ciki dai Isra’ilar ta kafa wani kwamitin bincike domin bin diddigin lamarin, bisa fargabar kada hakan ya janyo mata rikicin diflomatsiyya.
Ministan tsaron kasar Benny Gantz, ya ce sunan nan suna duba batun.
A kwanan nan ne dai aka bankado labarin leken asirin da ake zargin kamfanin Isra’ila mai leken asiri na NSO da kuma Pegasus.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Shugaban kasar Iraki Barham Saleh da na cikin mutane dubu 50 da ake zargin an yi wa leken asiri da manhajar ta Pegasus.