Dan wasan gaba na Manchester City Raheem Sterling da kwantiraginsa ke shirin karewa a shekarar 2023 ya ce tun daga yarinta ya na fatan ganin ya take leda a wajen Ingila karkashin wata gasar wadda ba Firimiya ba.
A cikin makon nan dai Raheem terling ya ki amincewa da tsawaita kwantiraginsa da Manchester City ta yi masa tayi bisa sharadin dole sai idan zai ci gaba da kasancewa a jerin ‘yan wasa ajin farko da za a fara kowanne wasa da shi.
City dai ta yi amfani da Sterling a dukkanin wasanninta na Firimiya cikin wannan kaka, kazalika ya na cikin tawagar lokacin da suka sha kaye hannun PSG cikin watan jiya karkashin gasar cin kofin zakarun Turai.
Raheem Sterling wanda Man City ta sayo daga Liverpool cikin shekarar 2015 ya taimaka wajen karfafa kungiyar inda suka dage kofunan firimiya 4 na FA guda duk da cewa kungiyar ta gaza lashe kofin zakarun turai.
Raheem Sterling ya ce, Real Madrid kayatacciyar kungiya ce, amma ya jaddada cewa, yana samun farin ciki a Manchester City, inda yake taka ledarsa.
A yayin zantawa da jaridar AS ta Spain, Sterling ya ce, a halin yanzu akwai kwantiragi tsakaninsa da Manchester City kuma dole ne ya mutunta wannan yarjejeniyar a cewrasa.
A ranar Laraba mai zuwa ne Manchester City za ta kece raini da Real Madrid a Gasar Zakarun Turai, sannan su sake haduwa a ranar 17 ga watan gobe a Etihad zagaye na biyu a matakin kungiyoyi 16.