Ragowan Sojojin Faransa Na Tawagar Barkhane Sun Fice Daga Mali.
Sojojin Faransa da suka rage a cikin tawagar Barkhane, sun fice a hukumance daga kasar Mali, watanni shida bayan sanarwar da shugaba Macron ya bayar na cewa sojojin zasu bar kasar.
Tuni sojojin suka keta iyaka zuwa Jamhuriyar Nijar, wanda kuma ya kawo karshen kasantuwarsu na tsawon shekara 9 da rabi a Malin.
Ragoyan sojojin su kimanin 300 sun kasance a Malin domin tabbatar da tsaro a sansanin sojin Gao har zuwa lokacin mika shi ga rundinar sojin Mali, a cewar wata sanarwa da ma’aikatar tsaron kasar ta fitar.
Matakin dai na zuwa ne bayan wa’adin da wasu bangarorin al’ummar Gao suka dibarwa sojojin na faransa na su tattara su fice daga kasar cikin sa’o’I 72.
Daga kafin hakan an jima da ake ta zanga zangar kin jinin sojin na faransa a Mali, har zuwa lokacin da sojojin dake mulki a kasar suka raba gari da da faransa wacce ta yi wa kasar mulkin mallaka.
Sansanin sojin Gao, shi ne mafi girma na sojojin faransa a Afrika.
Faransa dai ta rasa sojoji 59 a tsawon shekarun da tawagarta ta kwashe a kasar ta Mali, kana kuma ta kashe kudade da yawansu ya kai biliyan 5 Yuro a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2020.