Kusan falasdinawa miliyan 1.4 ne sakamakon rasa matsunan su suka gudu Rafah garin dake makotaka da Egypt.
Sojojin Isra’ila sun gudanar hare hare ta sama a Rafah bayan sun bayar da kashedin aiwatar da hakan a kan falasdinawa kusan miliyan 1.4 dake gudun hijira a muhallin sakamakon tashe tashen hankulan dake faruwa a Gaza.
A kusan watanni shidda da akayi ana ruwan wuta a Gaza, hakan ya kusan yin sanadin rushewar Gaza gabadaya kuma ya kusa sanya yankin a halin fari, kamar yadda majalisar dinkin duniya ta tabbatar.
Yanzu kuma hankalin duniya ya koma kan yankin Rafah wanda yakin kasa da Isra’ila ke son kaiwa na iya fantsama daruruwan dubunnan mutane zuwa gurare mabambanta.
Birni na karshe wanda sojojin kasan Isra’ila ba su shiga ba a fadin Gaza shine Rafah kuma shine hanya guda daya wacce taimakon gaggawa kan isa ga yankin Gaza daga kasashen makota idan bukatar hakan ta taso.
Isra’ila tayi barazanar cewa zata fadada ayyukan sojin ta na kasa zuwa yankin Rafah idan ‘yan gwagwarmayar Hamas basu saki sauran Isra’iliyawan da take rike da su ba zuwa watan ibada na Ramadan wanda zai kama a March Mai zuwa.
See Also: Me Ya Faru Da Alkawuran Bin Salman?
Kamar yadda kafar sadarwa ta Al-Jazeera ta rawaito ma’aikatar lafiya ta Gaza ta tabbatar cewa, ranar alhamis kisan mutane 99 wanda akasarin su mata, kananan yara da tsofaffi ne.
Adadin wadanda suka rasa rayukan tun daga 7 ga September ya kai 29,410 yayin da wadanda suka ji raunuka suka kai
adadin 69,465.