Raeisi Mun Zo Katar Ne Don Qarfafa Dankon Zumunci Da Makobta Kasashe Yankin Tekun Farisa.
Shugaban kasar Iran wanda yake ziyarar aikin na kwanaki biyu a kasar Qatar ya bayyana cewa manufar ziyararsa zuwa kasar Qatar itace, karfafa dankon zumunci, makobtaka da kuma dibliomasiya da kasashen yankin tekun farisa.
Kamfanin dillancin labaran IP ya nakalto shugaban yana fadar haka kafin ya bar Iran zuwa birnin Doha a safiyar jiya Litinin. Ya kuma kara da cewa za’a kulla yarjeniyoyi da dama don karfafa tattalin arzikin kasashen biyu.
Har’ila yau shugaban ya halarci taron kungiyar kasashe masu arzikin gas a duniya wanda aka fara a yau Talata a birnin Doha na kasar Qatar.
Shugaban ya ce ya je kasar Qatar ne bisa gayyatar Sarki Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, kuma yana fata, tare da hadin kai da kasar Qatar Iran zata fadada ayyukan hakar iskar gas da ke kan iyakar kasashen biyu.
Tuni dai an rattaba hannu kan yarjeniyoyi 14 tsakanin kasashen biyu. Yarjeniyoyin sun hada da ta bangaren tattalin arzikin da kuma makamashi.