Harin da sojojin Isra’ila suke kaiwa Raafah zai jefa rayuwar dubban Falasdinawa cikin hadari kuma zai zama babbar illa ga ayyukan jinƙai a yankin baki daya, in ji ofishin jinƙai na Majalisar Dinkin Duniya.
Isra’ila ta yi gargadin kai farmaki kan kungiyar Hamas a kudancin birnin Raafah da ke kudancin Gaza, kimanin mutum miliyan daya da suka rasa matsugunansu suke cunkushe a raafah suna samun mafaka ta wucin gadi, bayan da Isra’ila ta kwashe watanni tana kai hare-hare.
Mai magana da yawun ofishin jinƙai na Majalisar Dinkin Duniya Jens Laerke a wani taron manema labarai na Geneva ya ce “Zai iya zama kisan gilla na fararen hula da kuma zama tarnaƙi ga ayyukan jinƙai a yankin baki daya.”
Majalisar ministocin Isra’ila ta ɗage kaɗa ƙuri’a kan matakin dakatar da gidan talabijin na Aljazeera a kasar har zuwa ranar Lahadi mai zuwa, kamar yadda kafafen yada labarai na cikin gida suka ruwaito.
Shafin intanet na Walla na Isra’ila ya bayyana cewa, majalisar ministocin kasar ba ta kaɗa ƙuri’a a taron da ta yi da yammacin ranar Alhamis kan matakin rufe tashar Aljazeera a Isra’ila.
“Majalisar zartaswar, wacce ta gana da yammacin ranar Alhamis, ya kamata ta kada kuri’a kan shawarar da Firaiminista Benjamin Netanyahu da Ministan Sadarwa Shlomo Karhi suka yanke na haramta ayyukan Al Jazeera a Isra’ila, amma a minti na karshe, an dage zaben,” in ji shafin intanet din.
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinu Hamas ta yi kira ga ƙasashen duniya da su ɗauki mataki don “hana” cin zarafin da Isra’ila ke yi kan ‘yan jaridar Falasdinu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya, Hamas ta ce: “Muna kira da a dauki matakin yin Allah wadai da fallasa da kuma aikata laifukan keta hakkin mamaya, da kuma kare ‘yan jaridu a Falasdinawa da kwararrun kafafen yada labarai daga zalunci da ta’addanci na mamayar.
Kungiyar Falasdinu ta tabbatar da cewa “lafukan da Isra’ila ke yi wa ‘yan jarida ba za su boye gaskiyar ta’addanci da cin zarafi ba”.
Hamas ta jaddada cewa Isra’ila ta “kasa ɓata Falasdinawa a idon ƙsashen Larabawa da na Musulmai da ma na sauran ƙasashen duniya”.
DUBA NAN: Kwamitin Tuntuba Kan Gaza Ya Soma Zama
Aƙalla ‘yan jarida 141 ne suka mutu, wasu fiye da 70 kuma suka sami raunuka sakamakon harbin da sojojin Isra’ila suka yi musu, baya ga kama wasu da dama a yakin da Isra’ila ke ci gaba da yi a Zirin Gaza tun ranar 7 ga Oktoba, 2023, in ji ofishin yada labaran gwamnatin da ke Gaza.