Quds; Yahudawan Sahyuniya Sun Auka Kan Masallata A Masallacin Al-aqsa.
Dakarun gwamnatin sahyoniyawan sun kai hari a safiyar yau 29 ga watan April a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan ranar Quds a masallacin Al-Aqsa inda suka yi arangama da Falasdinawa masu ibada.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a rahoton jaridar Quds Al-Arabi, a yayin farmakin sojojin gwamnatin mamaya sun yi ta harbin kan mai uwa da wabi a kan Falasdinawa, sannan kuma matasan Falasdinawa sun yi ta jifa da duwatsu domin kare kansu.
‘Yan sandan yahudawan sahyuniya sun kuma hana matasa masu ibada shiga masallacin, kuma shaidun gani da ido sun ce an jikkata wasu Falasdinawa a wurin.
Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta bayar da rahoton cewa, Falasdinawa 12 ne suka jikkata a rikicin masallacin Al-Aqsa kuma an ba su agajin gaggawa sannan aka kai su asibitin Al-Maqassid.
READ MORE : Jagora; Kowace Rana ranar Quds Ce Matukar Dai Yahudawa Suna Mamaye Da Masallacin Al-aqsa.
Tun a ranar Juma’ar da ta gabata daruruwan Falasdinawa ne suke gudanar da addu’o’i a masallacin Al-Aqsa, kuma a safiyar yau daruruwan Falasdinawa ne suka shiga masallacin Al-Aqsa suna kabbara domin gudanar da sallar Juma’a a masallacin a ranar Juma’ar karshe ta watan Ramadan, lokacin da ‘yan mamaya suka kai musu hari.