Quds; Martani Kan Hare-Haren Isra’ila A Kan Masallacin Aqsa.
Kungiyoyin Hamas da Jihad Islami sun yi Allawadai da harin yahudawan Isra’ila a kan masallacin Aqsa.
Bayan laifuffukan da yahudawan sahyuniya suka yi a yau na raunata Falasdinawa da dama a masallacin Al-Aqsa, kungiyar Hamas da Jihad Islami sun yi Allah wadai da wadannan abubuwa tare da jaddada cewa sakamakon wadannan laifuffukan ya rataya ne a kan wuyan gwamnatin sahyoniyawan.
Kungiyar Islamic Jihad ta Falasdinu ta sanar a safiyar yau Juma’a cewa harin da aka kai kan masu ibada a Masallacin Al-Aqsa laifi ne da ‘yan mamaya ke da alhakinsa.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce harin da aka kai kan masu ibada wani yunkuri ne da bai yi nasara ba na fitar da masu ibada daga masallacin Al-Aqsa da nufin cin mutuncin musulmi .
Kungiyar ta kara da cewa: Makiya sun gane cewa wutar da suka kunna za ta koma gare su ta kone su.
Har ila yau Jihad Islami ta bayyana cewa idan ‘yan mamaya ba su daina aikata laifukan da suke aikatawa a masallacin Al-Aqsa ba, arangamar za ta kasance kusa da wuya fiye da yadda suke zato.
A nasa bangaren Saleh al-Arouri, mataimakin shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas, ya jaddada cewa duk wani kutse da Isra’ila ke yi kan masallacin Al-Aqsa zai kara dagula al’amura a yankin baki daya.
Ya ce al’ummar Falasdinu a shirye suke a kowane lokaci domin tunkarar ‘yan mamaya na Isra’ila, kuma Palasdinawa za su shiga wani sabon salon tinkarar mamayar daga yammacin kogin Jordan da birnin Quds.
Mataimakin shugaban ofishin siyasa na kungiyar ta Hamas ya kara da cewa: “Ba a yaudare mu da alkawuran makiya, kuma mun yi imani da karfi da kuma shiri da al’ummarmu ke da shi na kare masallacin Al-Aqsa da dukkan abin da Allah ya hore mana.”