Shugaban Rasha Vladimir Putin ya sha alwashin ci gaba da zafafa mamayarsa a kan Ukraine, a yayin da shugaba Volodymyr Zelensky ke neman taimakon soji daga kasashen yamacin duniya, duk da cewa bangarorin biyu sun yi ganawar lalubo yarjejeniyar tsagaita wuta a Alhamis.
Macron
Fadar gwamnatin Rasha ta Kremlin ta ce bayan ganawarsa da shugaba Emmanuel Macron na Faransa, Putin ya ce Rasha za ta ci gaba da dauki- ba- dadi da wadanda ya kira masu tsananin kishin kasa da ke dauke da makamai.
NATO
Saboda haka ne shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya yi kira ga kasashen yammaci su kara wa kasarsa taimakon soji, bayan da kungiyar tsaro ta NATO ta ce ba za ta sanya dokar hana zirga-zirgar jiragen sama ba, don kauce wa barkewar yaki na kai tsaye da kasar Rasha mai tarin makaman nukiliya.
EU
Tarayyar Turai ta ba wa Ukraine din jiragen yaki, kana wata majiya ta ce gwamnatin Jamus na shirin aikewa da karin makaman kakkabe jiragen saman yaki 2,700 zuwa Ukraine.
Mamayar da yanzu ta shiga mako na 2, ta mayar da Rasha saniyar ware a bangaren hada-hadar kudi, diflomasiyya, wasanni da al’adu a duniya.