Putin ya ki ya gana da Ukrain a wata kasa idan ba Bilarusia ba.
Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa; Shugaban kasar ta Rasha Vladimir Putin ya ki yarda da ya gana da takwaransa na Ukiraniya Volodymyr Zelenskyy a birnin Kudus ko wata kasa idan ba Bilarusia ba.
HKI dai ta shiga cikin masu shiga tsakanin yakin da ake yi a tsakanin Rasha da Ukireniya, kamar yadda kasashen Turkiya, jamus da Faransa suke yi.
A lokacin harin da HKI ta rika kai wa a yankin Gaza a shekarar da ta gabata, shugaban kasar ta Ukireniya yana cikin na sahun gaban wajen goyawa ‘yan sahayoniyar baya da bayyana abinda suke yi akan al’ummar Palasdinawa da cewa kare kai ne.