Putin; Duk Kasar Da Ta Hana Shawagin Jirage, Ta Shiga Yakin Ukraine.
Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya gargadi duniya da cewa duk wata kasar da ta saka dokar hana shawagin jirage, yana nufin ta shiga yakin Ukraine.
Shugaban na Rasha yayin wani jawabi ya ce “Za mu dauki duk wani mataki da aka dauka ta wannan hanyar a matsayin shiga cikin yaki a kasar.”
Dama dai kungiyar tsaro ta NATO, ta ce irin wannan matakin zai iya rura wutar yakin zuwa wasu kasashe.
Shugaban Ukraine dai Volodymyr Zelensky ya caccaki Nato kan rashin ayyana hana shawagin jirage, yana mai danganta shi da “rauni da rashin hadin kai.”
A haklin da ake ciki dai an shiga kwana na goma na matakin sojin da kasar Rasha ta ce ta dauka kan Ukraine, a wani mataki da ta ce na kakkabe kasar ne daga ‘yan nazi.
Saidai matakin ja yanyo mata takunkumai marasa adaddi daga kasashen turai da kuma Amurka.