Putin; An Wuce Lokacin Da Wasu ‘Yan Tsirarun Kasashe Za Su Rika Juya Duniya.
Shugaban kasar Rasha Valadimir Putin ya bayyana cewa, lokaci ya wuce da wasu ‘yan tsirarun kasashe za su rika juya duniya yadda suka ga dama.
Putin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a gaban babban taron kasa da kasa kan harkokin tattalin arziki da aka gudanar a birnin Saint Petersburg na kasar Rasha karo na 25.
Shugaban an Rasha ya ce, kasashen turai sun tafka babban kure da suka biye ma Amurka wajen hankoron ganin sun cutar da Rasha, domin kuwa takunkuman da suke kakaba wa Rasha za su cutar das u matuka, kuma hakan zai haifar da manyan matsaloli na tattalin arziki da na zamantakewa a cikin kasashen turai.
Ya kara da cewa, sun saka ma Rasha takunkumi domin karya tattalin arzikinta, amma kuma sai lamarin ya zama akasi, domin kudin Rasha sun kara karfi a halin yanzu fiye da kowane lokaci a baya.
Dangane da ayyukan soji da Rasha ke gudanarwa a Ukraine, Putin ya ce komai yana tafiya kamar yadda aka tsara, kuma daukar wannan matakin shi ne daidai domin kare tsaron Rasha daga barazanar kasashen da ke yin amfani da Ukraine, da nufin cutar da Rasha da al’ummarta.
Sannan kuma ya kara da cewa, kasashen da suke daukar matakan adawa da gaba a kan Rasha, da mayar da ita sanaiyar ware, ya ce shi ma wannan matakin bai yi nasara ba, domin kuwa mafi yawan kasashen duniya a nahiyar Asiya da Afirka da Latin Amurka suna tare da Rasha, ya ce lokaci ya kawo karshe da Amurka da kasashen turai za su rika cin Karensu babu babbaka a kan kasashen duniya.