Shugaban Rasha Vladimir Putin ya kare hare haren da kasar ke kai wa Ukraine, inda ya zargi Ukraine din da kasashen yamma da neman rikici, a yayin da yake kokarin amfani da bikin tunawa da nasarar yakin duniya wajen neman goyon bayan al’umar kasar.
Da yake jawabi a wajen faretin shekara-shekara na tunawa da ranar nasarar Tarayyar Soviet a kan sojojin Nazi na Jamus, Putin ya ce dakarun Rasha da ke Ukraine su na kare martabar kasarsu ne, yana mai bayyana rikicin a matsayi ci gaban yakin duniya na 2.
Putin ya jaddada wa dakarun Rasha da ke fagen fama a Ukraine cewa su na yaki ne don tabbatar da makomar kasarsu, don kada kowa ya manta da darrusan yakin duniya na 2.
Putin ya yi ta kokarin danganta yakin Ukraine da abin da Rashawa ke kira ‘gagarumin yakin kishin kasa’ ta wajen bayyana hukumomin Ukraine a matsayin masu akidar Nazi na wannan zamani.
Bai yi wata sanarwa mahimmiya ba a yayin jawabin nasa, duk kuwa da yadda rahotanni suka nuna cewa yana iya amfani da bikin wajen gabatar da rincabewar rikicin.
A maimakon haka sai Putin ya ci gaba da kare abin da ya kira sintirin soji a Ukraine, yana mai cewa abokanta na Turai na shirya kullalliyar mamayar yankunan Rasha na tarihi, ciki har da yankin Donbas da crimea da ke amfani da harshen Rashanci, wadanda Rashar ta mamaye a 2014.
Putin ya ce Rasha ba ta da wani zabi face mayar da martani a kan tambayar da take tunani kasashen yamma za su iya yi mata ta hanyar mamaya, yana mai bayyana shi a matsayin mataki mafi dacewa da ya kamata ‘yantatar kasa mai karfi ta dauka.