Ga dukkanin alamu kungiyar Paris Saint Germain (PSG) ba ta son rabuwa da gwaninta Kylian Mbappe a nan kusa, duk da alakanta dan wasan da sauyin sheka zuwa Real Madrid da ake yi nan da ‘yan watanni, yayin da wasu daga cikin fitattun ‘yan kwallon kafa, tsaffi da na yanzu ke shawartarsa da ya gaggauta raba gari da gasar League 1.
A baya bayan nan, rahotanni daga kasar Faransa suka bayyana cewa PSG na shirin gabatarwa da Mbappe tayin sabuwar yarjejeniyar da za ta sanya shi zama dan wasan da ke karbar albashi mafi tsoka a duniya, inda zai rika amshe fiye da fam dubu 500 a duk mako, kwatankwacin naira miliyan 283 da dubu 204.
A karshen kakar wasa ta bana yarjejeniyar Mbappe da PSG za ta kare inda zai shafe fiye da shekaru 4 a kungiyar.
Real Madrid dai ba ta taba boye aniyar sayen Mbappe ba, wanda ta so fara tattaunawar baka da shi tun a watan Janairu, bayan da ta gabatar da tayin Euro miliyan 220 ga PSG kan dan wasan nata a lokacin bazara na shekarar 2021.
Zuwa yanzu kwallaye 154 Mbappe ya ci wa PSG kwallaye a wasanni 203 da ya bugawa kungiyar tun daga shekarar 2017.