Fira Ministan Birtaniya Boris Johnson ya amsa laifin karya dokar hana fita ta hanyar halartar wani bikin rawa a fadar gwamnatin kasar a daidai lokacin da dokar hana zirga zirga ke aiki domin dakile yaduwar cutar Korona (Partygate)
Matakin na Fira Minista Johnson ya biyo bayan fitar da wani rahoto na cikin gida kan abin kunyar da ya aikata da ake kira da “Partygate”.
Kawo yanzu dai Fira Ministan na Birtaniya bai nuna alamun sauraron kiraye-kirayen da masu suka ke yin a yayi murabus ba, saboda abinda ya aikata.Yan adawa sun bukaci Boris Johnson ya sauka daga mukaminsa.
Boris Johnson da Korona
A lokacin bullar cutar ta Korona,FiraMinistan Birtaniya ya kasance a asibiti na wani lokaci,Gwamnatin Birtaniya ta sanar da sallamar Firaminista Boris Johnson daga asibiti mako guda bayan an kwantar da shi sakamakon kamuwa da cutar Korona, wadda ta kai ga ajiye shi a gobe da nisa na kwanaki 3.
A wani labarin na daban biritaniya ta ce ta ware Pam biliyan daya kwatankwacin Dalar Amurka biliyan daya da miliyan dari uku, na karin tallafi ga ‘yan kasuwa da suka fi fama da kalubale saboda sabon nau’in Omicron na cutar Korona.
Ministan kudi Rishi Sunak ya ce yana da kwarin gwiwar cewa matakan za su taimaka wa dubban ‘yan kasuwa, amma ya ce akwai bukatar daukar matakai masu tsauri, idan har gwamnati na son tunkarar nau’in na Omicron, wanda zai iya yin illa ga tattalin arzikin kasar.
Tallafin da aka fitar, kamfanonin shakatawa a Ingila za su karbi Pam 6,000 ga kowane wuri da suke da shi, wanda ya kai kusan fam miliyan 700 na sabon kunshin.
Ma’aikatar Kudin kasar ta ce tallafin dai ya yi daidai da wanda aka bai wa ’yan kasuwar da ke karbar baki da yawon bude idanu, lokacin da aka rufe kasuwacinsu gaba daya a farkon shekarar 2021.
Asusun tallafawa kungiyoyin al’adu zai karbi Pam miliyan 30, yayin da za a ba da fam miliyan 100 ga hukumomin lura da al’amuran cikin gida na Ingila don inganta shirin tallafin kasuwanci sai kuma Pam miliyan 150 da aka warewa gwamnatocin Scotland, Wales da Ireland ta Arewa.
Biritaniya ta karbi rancen sama da Pam biliyan 300 a cikin shekarar da ta gabata don magance matsalar tattalin arzikin da annobar Corona ta haifar, bayan tsaurara dokar kulle a kasar