Kamar yadda ma’aikatar lafiya ta kasar Palestine ta, sanar sojojin share wuri zauna na Isra’ila sun kashe falasdinawa arba’in da biyu a wannan shekarar cikin su har da yara kanana tara.
Ma’aikatar lafiyan ta Palestine a ranar larabar da ta gabata ta bayyana cewa, adadin larabawa ‘yan falasdinun da sojojin Isra’ilan suka bindige daga farkon wannan shekarar ta 2023 ya karu zuwa 42, cikin su a kwai tsohuwa daya, kananan yara 9, guda takwas daga cikin su an kashe su ne a watan janairu kurum, kamar yadda shafin Wafa News Agency ya rawaito.
Rahoton ya bayyana cewa gwamnatin Isra’ila ta rubanya aikata laifuka kan Falasdinawa a wannan shekarar ta 2023 fiye da sauran shekararun da suka gabata, ya kuma kara da cewa wannan shekarar tazowa Falasdinawa da wani yanayi na rashin dadi sosan gaske.
Ma’akatar ta cigaba da cewa, shekarara da ta gabata sojojin gwamnatin Isra’ila sun halaka mutane 224 ciki har da kananan yara 53 da kuma mata 17 wannan ya tabbatar da shekarar 2022 a matsayin shekara mafi muni ga Falasdinawa tun bayan shekarar 2005.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, takwas daga cikin yaran da aka kashe suna kara da shekarar goma ne, 45 kuma suna tsakanin shekara 11-17, yara 108 daga shekara 18-29, mutane 27 kuma daga shekara 30-39 mutane 19 kuma daga shekara 40-49, mutane 11 kuma daga shekara 50-59, mutane biyar da aka kashe kuma suna sama da shekaru 60 ne.
Sojojin Isra’ila suna kai hari gidajen Falasdinawa ne kusan kullum bisa dalilin wai suna son kama wasu Falasinawa ne da suka ce wai masu laifi ne, harin da suke kaiwa kuma kusan kowanne lokaci yana karewa da arangama mai tada hankali da mazauna yankunan.
A watannin da suka gabata sojojin Isra’ila sun gabatar da hare hare kan garuruwan Falasdinawa wanda hakan yayi sanadin rasa rayukan gomomin Falasdinawa kuma wasu suka fada hannun sojojin Isra’ilan.
A wata sanarwa Falasdinawa wadanda ke cikin mawuyacin hali sun bukaci majalisar dinkin duniya da kuma kasashen musulmi su taimaka musu.