Akalla Palasdinawa 6,546 da suka hada da kananan yara 2,704 ne aka kashe tare da jikkata 17,439 a hare-haren da Isra’ila ta kai tun ranar 7 ga watan Oktoba, in ji ma’aikatar lafiya a Gaza da ke karkashin ikon Hamas a ranar Laraba.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya habarta maku cewa: Akalla Falasdinawa 6,546 da suka hada da kananan yara 2,704 ne aka kashe yayin da 17,439 suka jikkata a hare-haren da Isra’ila ta kai tun ranar 7 ga watan Oktoba, in ji ma’aikatar lafiya a Gaza da ke karkashin ikon Hamas a ranar Laraba.
Ma’aikatar ta ce a cikin sa’o’i 24 da suka gabata an kashe Falasdinawa 756 da suka hada da kananan yara 344 a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa.
Ma’aikatar ta ce “An yi kisan kiyashi a yankin kudancin zirin Gaza.” Da yake magana game da tsarin kiwon lafiya, ma’aikatar ta ce hare-haren sun yi nisa ne tare da lalata cibiyoyi 57, kuma an kashe ma’aikatan lafiya 73, kuma motocin daukar marasa lafiya 25 ba su iya gudanar da aiki a yanzu.
A wani labarin na daban basarake Mai daraja ta daya a Zamfara, Sarkin Maru Abubakar Mai Gari, ya tsallake rijiya da baya yayin kai masa hari da ‘yan bindiga sukai masa a gidansa da ke hedikwatar Karamar Hukumar Maru, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum hudu a fadar a jiya Alhamis.
‘Yan bindigar tun a ranar Laraba da ta gabata ne suka kai wa Sarkin harin har zuwa jiya Alhamis, inda suka ci karo da tawagarsa suka bude musu wuta.
Ganau wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana wa wakilinmu cewa, “’yan bindigar sun mamaye fadar Sarkin ne inda suka bude wuta ba kakkautawa a kokarinsu na kashe Sarkin, Allah ya tseratar da shi.
Amma nan take ‘yan bindigar suka kashe mutane hudu daga cikin akwai dogarinsa, suka jikkata wasu da dama kuma sun lalata motocin sarkin.
Haka kazalika yanzu haka gwamnatin jihar ta bada umarnin rufe kasuwar Maru nan take .
Jami’in huda da jama’a na rundunar ‘Yansandar Jihar zamfara, ASP Yazidu Abubakar ya tabbatar da faruwar harin, kuma ya bayyana wakilinmu cewa, yanzu haka jami’an tsaro ne ke tsare da fadar Sarkin kuma mun baza jami’an tsaro lungu da sakon na Karamar Hukumar don tabbatar da tsaro.
Source: ABNAHAUSA