Pakistan Mutane sun kashe wanda ake zargi da ƙona shafukan Ƙur’ani.
Wani taron mutane sun kashe wani mutum da ake zargi da ƙona shafukan Ƙur’ani mai tsarki a yankin tsakiyar Pakistan, a cewar ƴan sanda, a wani lamari na rikici mai alaƙa da aikata saɓo na baya-bayan nan da ya faru a ƙasar.
Ƴan sanda sun ce an kama fiye da mutum 80 da ke da hannu a kisan a ranar Asabar a gundumar Punjab da ke yankin Khanewal.
Rahotanni sun ce mutumin yana tsare a wajen ƴan sanda ne kafin daga bisani mutane suka sato shi.
Tuni aka miƙa gawarsa a hannun iyalansa tun a ranar Asabar ɗin har ma an yi masa jana’iza.
Firaministan Pakistan Imran Khan ya ce za a duba lamarin cikin bin dokokin shari’a, sannan ya nemi a ba shi rahoto kan jami’an ƴan sandan da ake zargi da gaza yin aikinsu don ceton mutumin.
Ya ce gwamnatinsa “ba za ta lamunci barin mutane suna ɗaukar doka a hannunsu ba”.
Wani jami’in ɗan sanda Munawar Hussain ya ce jami’ai sun tafi neman mutumin da rahotanni suka ce shekararsa 40, suka gano shi ba a cikin hayyancinsa ba ɗaure a jikin wata bishiya.
- Ƴan sanda na neman bokan da ya caka wa mace ƙusa a kanta
- Zanga-zanga ta barke kan kashe mutumin da ya yi ‘ɓatanci’ ga Annabi Muhammad
- Malala ta ce ba ta fahimci aure ba sai da ta shiga ɗakin miji
Garin Khanewal yana da nisan kilomita 275 ne daga kudu maso yammacin Lahore.
“Mutanen ƙauyen ɗauke da makamai kamar su adda da rodi ne suka kashe mutumin tare da rataye gawarsa a jikin wata bishiya,” kamar yadda Mr Hussain ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Munawar Gujjar, babban jami’in ƴan sanda na reshen Tulamba, inda lamarin ya faru, ya ƙara da shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa, mutumin yana fama da lalurar taɓin hankali tsawon shekara 15 da suka gabata.
Kisan nasa na zuwa ne bayan wata biyu da kashe ma’aikacin wani kamfani ɗan Sri Lanka tare da cinna masa wuta da mutane suka yi kan zarginsa da aikata saɓo a birnin Sialkot a gundumar Punjab.
Dokokin aikata saɓo na Pakistan sun ƙunshi yanke hukuncin kisa ga duk wanda ya zagi Musulunci, amma masu suka na cewa ana amfani da su wajen cin zalin sauran mabiya addinai da ba su da yawa a ƙasar.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam da dama sun ce ana amfani da dokokin wajen yanke hukunci kan wasu abubuwan da ba su da alaƙa da addini kwata-kwata.