Pakistan; Miliyoyin Mutane Na Zanga-Zangar Adawa Da Tsige Imran Khan.
Tun bayan sanar da tsige Firayi ministan kasar Pakistan da majalisar dokokin kasar ta yi a jiya Lahadi, miliyoyin mutane ke ci gaba da gudanar da zanga-zanga a birnin Islam-abad da ma wasu biranen kasar, domin adawarsu a kan daukar wannan mataki da majalisar ta yi.
Rahotanni sun ce sama da birane 30 ne aka gudanar da zanga-zangar, inda ake ganin hakan zai bude wani sabon shafin dambarwar siyasa a kasar Pakistan, musamman ma yadda jama’a da dama daga cikin magoya bayansa suke zargin cewa Amurka da wasu kasashen turai suka kulla masa makarkashiya domin ganin bayansa.
A yau Litinin ne ‘yan majalisar dokokin kasar za su yanke shawara a kan wanda zai gaji Imran Khan, wanda aka cire daga mukaminsa na firaminista a kuri’ar yanke kaunar da aka kada bayan abokan hadakar gwamnatinsa sun juya masa baya, suna masu zarginsa da kasa warware matsalar tabarbarewar tattalin arzikin kasa, da kuma gaza cika alkawuran da ya dauka.
Yanzu haka dai jagoran ‘yan hamayya Shehbaz Sharif, wanda dan uwan tsohon firaministan kasar Nawaz Sharif ne ake ganin zai gaji kujerar firaministan.
Tun kafin wanann lokacin dai Imran Khan ya bayyana cewa, Amurka ta yi masa barazanar tumbuke gwamnatinsa, saboda yaki amincewa ta kafa sansanin sojojinta a cikin kasar Pakistan.