Kungiyar agaji ta Oxfam ta yi gargadin cewa rikicin Russia da Ukraine da kuma tasirin annobar korona ka iya jefa mutane miliyan 250 cikin tsananin talauci da yunwa.
Sabon alkaman na kungiyar ta Oxfam na nuna cewa mutane miliyan 263 a duniya na cikin halin bakin talauci, wanda ke karuwa saboda yakin Russia da Ukraine yayin da dama suka fara fama da shi sakamakon cutar Corona.
A cewar hukumar, bayan bakin talaucin da mutanen ke fuskanta musamman a kasashe masu fama da talauci na kara ta’azzara, yayin da ta kara da cewa wasu mutanen miliyan 63 na cikin hadarin gamuwa da kazamin talaucin, idan aka yi la’akari da tashin farashin kayayyaki da na makamashi a duniya.
Hukumar ta kuma ce idan aka yi la’akari da wannan alkalma to idan ba’a yi hattara ba mutane miliyan 860 ka iya fadawa cikin bakin talaucin da zasu yi wuyar fita, a don haka ne kungiyar ta bukaci hukumomin kudi na duniya da su gaggauta daukar matakan da suka dace.
Haka kuma Oxfam tabukaci a soke basukan da manyan bankuna da kasashen duniya masu arziki su ke bin mataulatan kasashe, yayin da ta bukaci a karawa kasashe da dai-daikun mutane da ke da arziki yawan kudaden harajin da ake karba.