Mai yiwuwa fitacciyar ‘yar tseren gudu ta Najeriya, Blessing Okagbare, ba za ta daukaka kara kan hukuncin dakatar da ita daga wasanni na tsawon shekaru 10 da hukumar kula da tantance nagartar ‘yan wasan motsa jiki AIU ta yi mata ba, kan amfani da haramtattun kwayoyi masu kara kuzari.
Haramcin karin shekaru biyar na wasanni kuma ya hau kan ‘yar tseren Najeriyar ne saboda samunta da laifin kin ba da hadin kai ga masu bincike.
Cikin wani sako da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta Okagbare ta ce lauyoyinta na nazarin matakin da za su dauka a nan gaba.
A halin yanzu dai wa’adin kwanaki 30 da suka ragewa ‘yar Najeriyar domin daukaka kara na gaf da cika.
A wani labarin na daban Tauraruwar tseren Kenya Agnes Tirop ta kwanta dama ranar Laraba, bayan da aka daba mata wuka a gidanta dake Iten.
Wata sanarwa da hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta Kenya ta fitar da ke tabbatar da afkuwar lamarin ta ce, ta nuna takaicin mutuwar Agnes Jebet Tirop wanda ta lashe kambun tagulla na duniya a tsaren mita dubu 10.
Humomin kasar suka sun tsinci gawar ‘yar tsaren a gidansu da ke Iten bayan da mijinta ya caka mata wuka. Amma har yanzu suna gudanar da bincike don gano ƙarin cikakkun bayanai game da mutuwar ta. ”
Tirop ta kafa tarihi ta hanyar lashe gudun fanfalaki na duniya a shekarar 2015, wanda ta zama matashiya na biyu da ta lashe kambin.
Ta kuma lashe tagulla a tsaren duniya a shekarar 2017 da 2019 a tseren mita 10,000.