Amurkawa da adadin su ya kai dubunnai ne suka cika titunan Oakland na yankin California domin nuna damuwar su dangane da yanayin yadda ‘yan sanda ke zaluntar marasa gata musamman bakaken fata, sa’annan su bukaci ayi wa bakar fatan nan Tyre Nicholes adalchi wanda ‘yan sandan Memphis suka kashe.
Wata kungiyar fada da ayyukan ta’addancin ‘yan sanda mai suna “Anti-Police-Terror Project” ne suka shirya zanga zangar a garin Oakland bayan wani bidiyo da aka yada ranar juma’a inda aka nuna ‘yan sandan Memphis guda biyar suna duka, mangari gami da watsawa Nicholes barkonon tsohuwa bayan wani abu da ya faru.
Wadanda sukayi magana a wajen zanga zangar sun hada da iyalan wadanda ‘yan sanda suka taba kashewa kuma sunyi Allah wadarai da takurawa babaken fata da ‘yan sandan ke yi.
Nichols wanda bakar fata ne, ya rasu kwana 7 bayan yasha duka a hannun ‘yan sanda, iyalin sa sun bayyana ya gamu da ‘yan sandan ne bayan ya dawo daga daukar hoton yadda rana ke faduwa.
Takurawar ‘yan sanda ga bakaken fata ko mutanen yankin asiya a Amurka na cigaba da karuwa wanda hakan ke sanda tsoro da dar dar a zukata.
Ko a watan mayun shekarar 2020 ma biyo bayan kisan bakar fata Geoge Floyd da ‘yan sanda sukayi ya janyo zanga zanga a birane da dama na Amurka harma da wasu kasashe.
Floyd wanda bakar fata ne dan shekara 46 ya gamu da ajalin sa ne a hannun wani dan sanda farar fata wanda ya danne masa wuya da gwuiwa a wani yanayi.
Bidiyon yadda abin ya faru ya nuna dan sandan ya danne wuyan Floyd ta baya na kusan mintuna tara a yayin da bakar fatan ke neman agaji, hakan ya harzuka mutane suka fita zanga zanga zanga a manyan birane.
A cikin wannan yanayi ne a birnin Washington DC lamarin ya zama na tashin hankali inda masu zanga zangar suka fusata suka kone wasu bangarori na birnin a ranar 31 ga watan mayu 2020