Isra’ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla huɗu fararen-hula a yankin Tal al Sultan da ke Rafah, a yayin da ta kai sabon hari a sansanin Nuseirat da ke tsakiyar Gaza da kuma arewacin Gaza bayan Nuseirat din, kamar yadda ganau suka shaida wa TRT World.
Zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa ta ɓarke a wasu biranen Amurka
Masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa sun toshe manyan hanyoyi a jihohin Illinois, California, New York da Oregon, lamarin da ya haddasa tarnaƙi ga masu zuwa Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Chicago O’Hare, da gadojin Golden Gate and Brooklyn da ma hanyar West Coast mai cke da hada-hadar jama’a a yayin da Isra’ila ke ci gaba da mamaye Gaza.
A Chicago, masu zanga-zanga sun toshe manyan hanyoyin da ke zuwa filayen jiragen sama da misalin ƙarfe bakwai na safe, a wani mataki da suka bayyana a matsayin “matsin lamba ta fuskar tattalin arziki domin ganin an bar Falasɗinawa sun sarara,” a cewar Rifqa Falaneh, ɗaya daga cikin mutanen da suka jagorancin zanga-zangar.
An katse tafiye-tafiye a birnin San Francisco na tsawon awanni a yayin da masu gangami suka toshe duk wasu manyan hanyoyin mota da na ƙafa da mahaya babura zuwa gadar Golden Gate Bridge inda suka kafa diram-diram cike da ƙasa da siminti suka toshe babbar hanyar Interstate 880 da ke Oakland.
DUBA NAN: APC Ta Kori Ganduje Bisa Zargin Cin Hanci Da Rashawa
Masu zanga-zanga da suka yi tattaki a Brooklyn sun toshe hanyar da ke isa Manhattan daga kan Gadar Brooklyn. A yankin Eugene na Oregon, masu zanga-zanga sun toshe hanyar Interstate 5, inda suka kawo tsaiko a tafiye-tafiye na fiye da minti 45.