NUPENG Ta Baiwa Yan Kasuwa Wa’adin Sao’i 24 Da Su Maido Da Farashin Mai Zuwa N165
Kwamare Afolabi Olawale sakatare janar din Kungiyar NUPENG ya fadi cewa mun baiwa yan kasuwar mai wa’adin sao’I 24 da su mayar da farashin man fetur zuwa N165 kan kowacce lita ko kuma mu sanar da sunayensu da kuma kunyata su a matsayin makiya ci gaban Alumma bayan wasu takunkumi da za su biyo baya.
Wannan mataki ya zama tilas ganin yadda ake ci gaba da ganin doyana layuka a gidajen mai a fadin kasar, tare da yin amfani da karancin kai din wajen muzgunwa masu ababen hawa,
Yace kungiyar NUPENG ba za ta ci gaba da zuba ido tana ganin wasu na amfani da wata dama suna cutar da alumma da ma kasa ba, don haka muna kira da alumma da su kasance tare damu a duk irin mataken da muka dauka domin kawo karshen wannan rashin tausayin.
Game da batun bayani da kamfanin mai na kasa ya fitar na irin ci gaban da aka samu na samar da manfetur Garba-deen Mohammad Yace: “kamfanin NNPC ya sanar cewa yana da wadataccen mai da ake bukata kuma sun dauki mataki kan matsalolin da suka kawo cikas wajen raba manfetur din da dangoginsu