Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labarai na kungiyar gwagwarmaya a kasar Iraki ta Nujba cewa, kakakin kungiyar Nasr Al-shummari Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labarai na kungiyar gwagwarmaya a kasar Iraki ta Nujba cewa, kakakin kungiyar Nasr Al-shummari ya bayyana abin da yake faruwa a kasar Afghanistan da cewa darasi ne ga kawayen Amurka a duk inda suke.
Injiniya Nasr Al-shammari ya ce, a lokacin da aka shirya wa kasar Iraki makirci aka turo ‘yan ta’addan Daesh daga kasashen duniya domin su mamaye kasar ad sunan kafa daular Khalifanci, idan da ba don sadaukarwar da rundunar sa kai ta al’umar Iraki Hashd Alshaabi suka yi ba, to da makomar Iraki za ta kasance kamar yadda Afghanistan ta zama ne a yanzu, da tun a shekara ta 2014 birnin Bagaza ya zama kamar yadda Kabul ta zama a 2021.
Ya ce wannan babban darasi ne da ya kamata kasashen da suke dogaro da Amurka bisa zaton cewa ita ce za ta kare su ko tabbatar musu da tsaro, da su sake tunani, musamman ma wasu daga cikin gwamnatocin larabawa, wadanda suka dogara da Amurka domin kare musu kujerunsu na sarauta, su kuma su yi ta mika mata daruruwan biliyoyin daloli.
Kungiyar Nujba dai babban reshe na dakaruin sa kai na al’ummar Iraki, wadanda suka taka gagarumar rawa wajen karya lagon ‘yan ta’addan takfir na Daesh a kasar Iraki.