Novak Djokovic zai rasa matsayin na lamba day ana duniya a wasan kwallon tennis bayan da ya sha kashi 6-4 7-6 (7-4) a hannun Jiri Vesely, a wasan daf da kusa da karshe na gasar Dubai Championships.
A ranar Litinin mai zuwa, za a maye gurbin dan kasar Serbia din da Daniil Medvedev a matsayin lamba daya na wasan kwallon Tennis na duniya.
Vesely, dan kasar Jamhuriyar Czech wanda shine lamba na 123 a duniya a wasann Tennis, ya bayyana mamakinsa da nasarar da ya samu a kan lamba daya na duniya.
Medvedev, dan kasar Rasha, zai kasance dan wasa na farko, wanda ba Novak Djokovic, Roger Federer, Rafael Nadal ko Andy Murray ba da ya haye zuwa wannan matsayi a cikin shekaru 18.
A wani labarin na daban Wasu shugabannin kasashen duniya sun caccaki matakin Rasha na mamayar Ukraine, inda kasashen yammacin Turai suka sha alwashin kakaba wa Rashar takunkuman karya tattalin arziki, a yayin da sakataren majalisar dinkin Duniya, Antonio Guterres ke bukatar kawo karshen rikicin da gaggawa.
Recep Tayyip Erdogan, Shugaban Turkiyya, wanda kasarsa mamba ce a kungiyar tsaro ta NATO, ya yi Allah wadai da matakin Rasha, yana mai bayyana shi a matsayin nakasu ga zaman lafiyar nahiyar.
A jawabin da ya gabatar ga al’ummar kasarsa, Firaministan Birtaniya, Boris Johnson, ya bayyana shugaban Rasha a matsayin dan kama-karya, wanda za a kakaba wa takunkumai sakamkon dirar mikiyar da ya yi wa ‘yanci da dimokaradiyya.
Shi ko sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres, bayan wani taron gaggawa na kwamitin tsaro, roko ya yi ga shugaban Rasha Vladimir Putin, yana mai kira a gareshi da ya kawo karshen hare hare don darajar ran dan adam.
Ministan harkokin wajen China, Wang Yi ya shaida wa takwaransa na Rasha Sergei Lavrov ta wayar tarho cewa kasarsa ta fahimci damuwar Rasha a kan batutuwan da suka shafi tsaro, kuma ya ja kafa wajen caccakarta