Babban manajar kamfanin NNPC na Najeriya Mele Kyari ya bayyana cewa kamfanin zai daina shigo da tataccen man fetur daga kasashen waje a shekara mai zuwa.
JONATHAN NDA- ISAIAH wakilin jaridar Leadership ta Najeriya ya nakalto Kyari yana fadar haka a hira ta musamman da ta hadasu. Ya kuma kara da cewa, yana fatan daga tsakiyar shekara mai zuwa ta 2023 Najeriya zata daina shigo da tataccen man fetur.
Kyari ya ce da farko kamfanin yana cikin aikin gyara don farfado da matatun man kasar guda ukku da yake da su, wato biyu a Wari sannan daya a kaduna. Wadanda a fadinsa idan sun kama aiki gadan-gadan zasu samar da miliyon 18 na tataccen man fetur.
Babban manajan ya kara da cewa yana fatan kafin haka matatan man fetur wanda kamfanin dan gwate yake ginawa zai samar da sauran tataccen man da kasar take butaka.
READ MORE : Iran; IRGC Sun Yi Karin Bayani Kan Yadda Suka Tsare Jiragen Ruwa Na Amurka.
Ya kammala da cewa matatan main a dan gote wanda kamfanin yake da kasha 20 cikin hannun jarinsa zai samar da lita miliyon 50 na tataccen man da kasar take bukata.