Nijar; Za A Yi Wa ‘Yan Ta’adda Afuwa Idan Suka Ajiye Makamasu Suka Rungumi Zaman lafiya.
Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya sake gabatar da bukatar yin afuwa ga masu dauke da makamai a kasar domin ganin sun sake komawa cikin al’umma domin gudanar da harkokin su na yau da kullum.
Yayin da yake jawabi ga jama’ar Makalondi dake Yankin Torodi kusa da iyakar Burkina Faso, shugaban yace koda yaushe kofar su a bude take domin karbar mutanen dake shirin watsi da wannan mummunar aikin kai hare hare suna kashe jama’a.
Bazoum yace muddin irin wadannan mutane suka yi watsi da ayyukan ta’addanci, suka kuma aje makaman su, gwamnati a shirye take ta tsugunar da su da kuma taimaka musu ta fuskar sana’a.
READ MORE : Putin; Rasha Za Ta Ragargaza Makaman Turawa Masu Cin Dogon Zango A Cikin Ukraine.
Shugaban ya shaidawa mutanen yankin cewar ba zai taba barin su ba, kuma zasu ci gaba da Nazari akan halin da suke ciki domin tabbatar da zaman lafiya kafin mayar damutane gidajen su.
READ MORE : Abdollahian; Matakin IAEA Na Adawa Da Iran Na Da Mummunan Tasiri A Makomar Tattaunawar Vienna.
READ MORE : Najeriya; Zaben Fitar Gwani Na ‘Yan Takarar Shugaban Kasa Na APC A Zaben 2023.