Kasashen na yammacin Afirka wadanda suka hada da Mali, Guinea da Burkina Faso sun goyi bayan juyin mulkin kasar Nijar lamarin da ke zama babbar barazana ga muradan kasashen yamma da kuma kokarin kungiyar ECOWAS na dakile wannan yunkurin
A baya bayan nan ma dai anyi juyin mulki a kasashen Burkina Faso da Mali biyo bayan yadda gwamnatocin kasashen suka kasa dakile matsalolin rashin tsaro
Juyin mulkin da aka dauki tsawon awanni 48 ba’a san halin da ake ciki ba wani Janaral na sojo Abdourahamane Tiani, ya bayyana kan sa a matsayin sabon shugaban kasa mandadin Muhammad Bazoum wanda aka hambare
Sai dai a zaman da ta gudanar ranar lahadin data gabata karkashin jagorancin shugaban ta Bola Ahmad Tinubu a Abuja ta cimma matsayar sanyawa Nijar din takunkuma masu yawa
Sa’annan ECOWAS ta bawa sojojin wa’adin sati daya da su mika mulki ga zababbiyar gwamnatin shugaba Muhammad Bazoum
Sai dai wani adadi mai yawa na mutanen Nijar sun fito zanga zanga domin nuna goyon bayan su ga sabuwar gwamnatin soji wacce ke ikirarin yanke duk wata alaka da faransa lamarin da bai yiwa Faransan dama kasashen yammacin turai dadi ba.
Wasu dai na zargin kasashen yammacin Turan da wawasar tattalin arzikin kasashen yammacin afrikan wanda hakan ya sanya rashin yarda gami da tsana ga turawan yamman a zukata akasarin mutanen kasashen yammacin Afrikan.
Shugaban kasar Faransa dai a wani bayani nasa, yayi barazanar daukan mataki mai tsauri idan muradan Faransan suka shiga wani yanayi a Nijar din.
Sai dai sabuwar gwamnatin Nijar ta nemi taimakon kasar Rasha domin taimaka mata ta cimma nasara gami da fita da matsalolin dake tattare da jaririyar gwamnatin wacce ke fama da barazana daga bangarori mabam anta.
Idan juyin mulkin Nijar ya karasa samun nasara ana iya cewa kasashen da suka bijirewa muradan kasashen yammacin turai sun karu kenan a yammacin afrika.