A yau Asabar ne tawagar Kungiyar ECOWAS ta sake komawa birnin Yammai na Jamhuriyar Nijar domin ganawa da mahukuntan sojoji na kasar.
Rahotanni sun ce tawagar ta isa Yamai ne karkashin jagorancin tsohon shugaban mulkin soji na Najeriya, Janar Abdusalami Abubakar, wadda ta hada da Sarkin Musulmin Najeriya Muhammad Sa’ad Abubakar da kuma wasu jami’an daga kasashe daban-daban na kungiyar.
Sabon Firaministan Nijar Ali Muhammad Lamine Zeine ya tarbi wannan tawagar a filin jirgin saman Yammai.
A lokacin da tawagar ECOWAS ta ziyarci Yamaia kwanakin baya ba ta iya samun damar ganawa da Janar Abderahmane Tchianeba kamar yadda kuma ba ta gana da hambararren shugaban kasar Bazoum Mohammed , amma a wannan karon dai ana sa ran za su gana da a cewar wasu majiyoyi.
Ziyarar dai tana zuwa bayan kammala zaman taron da manyan hafsoshin sojin kasashen ECOWAS suka gudanar ne a Ghana, inda suka ce sun ayyna ranar kai hari kan jamhuriyar Nijar domin dawo da gwamnatin da sojoji suka hambarar, matukar dai hakan ba ta yiwu ba tahanyoyin diflomasiyya.