Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar sun ce kungiyoyin fararen hula da dama sun shigar da kara kotu bisa korafin zurarewar kimanin dala Amurka miliyan 99 daga baitulmalin gwamnatin kasar.
Ali Idrissa na kungiyar ROTAB, ya ce kawancen nasu ya yanke shawarar garzayawa kotu ne bayan nazartar wani rahoto kan kashe kudaden gwamnati a shekarar 2021 da ta gabata, wanda aka mikawa shugaba bazoum Mohammed a watan Afrilun da ya gabata.
A cewar Idrissa sun gabatar da korafin nasu ne tun a ranar Larabar da ta gabata.
Cikin korafin nasu, gamayyar kungiyoyin fararen hular na nijar sun ce bincikensu ya gaza gano CFA biliyan 63 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 99 da basu gano yadda aka yi da su ba.
A wani labarin na daban Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci taimakon gaggawa daga masu bada agaji domin taimakawa ‘yan Nijar sama da miliyan biyu dake fama da matsalar karancin abinci da ambaliyar ruwa da kuma hare-haren ‘yan bindiga.
David Carden, jami’in kungiyar agaji ta Majalisar da ya ziyarci Nijar, yace suna bukatar akalla Dala miliyan 523 domin taimakawa mutane miliyan 2 da dubu 100.
Jami’in yace Nijar na fuskantar matsaloli da dama da suka hada da na jinkai da matsalar tsaro da kuma tashe tashen hankulan da Yan bindigar ke haifarwa wajen kai hari kan fararen hula abinda ya haifar da talauci a cikin jama’a.
Carden yace annobar korona ta dada jefa al’ummar kasar cikin mummunan yanayi inda suke bukatar taimako sosai, yayin da yaran dake tsakanin watanni 6 zuwa shekaru 5 a duniya da yawan su ya kai 457,200 ke fama da tamowa.
Jami’in yace ziyarar da ya kai kasar ta bashi damar ganewa idan sa halin da irin wadannan mutane ke ciki, yayin da kuma ya ziyarci Ouallam dake arewacin birnin Yammai inda Yan bindiga suka kasha fararen hula 100a kauyuka guda 2 ranar 2 ga watan Janairun da ta gabata.