Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum, ya jaddada kiransa ga mayakan kungiyoyi masu ikirarin jihadi da ke da burin tuba a yayin wata ziyarar da ya kai yankin kudu maso yammacin kasar, yana mai cewa kofa a bude take ga irin wadannan mayaka.
A gaban dimbim al’ummar Torodi, a kusa da kan iyakar kasar da Burkina Faso, shugaba Bazoum ya ce ya sha kira ga mayakan da ke ta’addanci da sunan jihadi da su bar rayuwa mara amfani da ba za ta tsinana musu komai ba.
Ya ce lallai idan suka yi watsi da ta’addanci, hukuma za ta karbe su zuwa cikin al’umma, ta kuma sama musu aikin yi don tabbatar da ci gabansu ta fannin tattalin arziki, yana mai bayyana fatan suna sauraronsa.
A karshen watan Fabrairu ne shugaban Nijar Mohamed Bazoum ya sanar da cewa ya fara tattaunawa da ‘yan asalin kasarsa da ke cikin kungiyar IS a wani yunkuri na lalubo zaman lafiya.
A wani labari na daban kuma wata kungiyar ta’addanci da ke Mali, mai alaka da Al-Qaeda ta dau alhakin harin da aka kai kasar Togo a watan da ya gabata.
Kungiyar Jama’at Nasr al-Islam wal Muslimin tana ta fadada ayyukanta a cikin ‘yan kwanakin nan, inda take barazana ga arewacin kasashen Benin, Ivory Coast, Ghana da Togo.
Gwamnatin Togo ta tabbatar da harin ta’adancin da ya auku ranar 11 ga watan Mayu a garin Kpekankandi, kusa da iyaka da Burkina Faso, inda ‘yan ta’adda ke da yawa.
Hukumomin Togo sun ce dakarun Togo 8 ne suka mutu, 13 suka samu raunuka.
Wata majiya daga gwamnatin Togo ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa kimanin mahara 60 bisa babura ne suka kai wa dakarun Togo hari.