Paris St-Germain ta gaza kare kambunta na gasar kofin kalubalen Faransa, wato French Cup a jiya Litinin , bayan da Nice ta doke ta a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Bayan da aka tashi wasan canjaras babu ci ne, sai Nice ta lashe wasan da ci 6-5 a bugun fenariti.
Mai tsaron raga Marcin Bulka, wanda Nice ta dauko aro daga PSG ne ya kama kwallon da ta kawo karshen fatan PSG na lashe kofin.
ya hana kwallon Xavi Simons shiga raga, lamarin da ya kai nice matakin daf da kusa da karshe, kuma za su fafata ne da Marseille.
Wannan rashin nasarar, koma baya ne ga kocin PSG Mauricio Pochettino, wanda ya fito da tawaga mai karfin gaske, ciki har da Lionel Messi da zummar lashe wasan.
A wani labarin na daban kuma Sabuwar Jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya a Myanmar ta bayyana damuwarta kan yadda tashe-tashen hankula ke kara ta’azzaara a kasar, yayin da ta bukaci tsagaita musayar wuta tsakanin sojoji da ‘yan adawar kasar.
Kawo yanzu, an gaza samun cikakkiyar matsaya wajen maganance rikicin kasar duk da yunkurin diflomasiyar da aka yi karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya da kuma Kungiyar Kasashen Kudancin Asiya.
Manyan Janar-janar na sojin Mynamar sun ki amincewa su yi zaman sulhu da bangaren ‘yan adawar kasar.
A jawabinta na farko tun bayan darewa kan sabon mukaminta, jakadiyar Majalisar Dinkin Duniyar a Myanmar, Noeleen Heyzer ta ce, ta kadu da abin da ke ci gaba da wakana a kasar musamman a jihar Kayin.
Ta kuma yi kira ga daukacin bangarorin kasar da su amince a isar da kayayyakin jin-kai ga mabukata da suka ha da wadanda suka tsere daga muhallansu.
A bangare guda, Kungiyar Save the Children ta tabbatar cewa, an kashe biyu daga cikin jami’anta a jajibirin ranar bikin Kirismati a wani kisan kare dangi da ake zargin sojojin Myanmar da aikatawa a kasar.