Neymar ya shaidawa manema labarai cewa, baya tunanin zai sake daukar shekaru a nan gaba yana kwallo.
Sai dai Pochettino ya alakanta kalaman na Neymar da tsantsar kankan da kai da ya ce dan wasan na da shi.
Acewar mai horarwar, Neymar mai shekaru 29 ya kan fadi kawai duk abin da ya zo ransa idan ya na gaban manema labarai, amma dan wasan na da sauran karfi da kuma gagarumar gudunmawar bayarwa a duniyar kwallo.
Neymar dan wasa mafi tsada a Duniya, da ya taka leda sau biyu a gasar ta cin kofin Duniya, shi ne dan wasa na biyu mafi zura kwallo a Brazil bayan Pele, kalaman nasa ya zama muhawara tsakanin magoya bayansa, ganin cewa lokacin da za a yi gasar cin kofin Duniya ta 2026 ya na da shekaru 36 ne kadai a Duniya, kasa da shekarun Ronaldo ko kuma Zlatan wadanda har yanzu suke nuna bajinta.