Neymar ne ya fara cin kwallo a wasan, ya kuma ci wa PSG kwallonta ta 5, wadanda duk Mbappe ne ya taimaka mai wajen saka su.
Kylian Mbappe ya ci kwallaye 2, kana ya taimaka aka ci 3 a wasan da Paris St-Germain ta ci gaba da jan ragamar teburin gasar Ligue 1 na Faransa da maki 12, bayan da ta doke Lorient da ci 5 -1.
A zubi na 2 na wasan, bayan hutun rabi lokaci Mbappe ya saka kwallo, wadda ta kai adadin kwallayen da ya ci zuwa 17, kafin daga bisani ya gyara wa Messi wata kwallo ya saka a raga.
Terem Moffi ya saka wa Lorient kwallo daya bayan hutu, amma rashin nasarar da ta samu na nufin cewa saura maki daya ta shiga jerin kungiyoyin da za su rikito daga teburin Ligue 1 na Faransa din
Saura kiris ma Mbappe ya ci kwallaye 3 rigis a wasan amma hakan bai yiwu ba a kusan karshen wasan.
A wani labarin na daban Magoya bayan Paris Saint-Germain a gasar Ligue 1 ta kasar Faransa, sun yi wa fitattun ‘yan wasan kungiyar da suka hada da Lionel Messi da Neymar ihu a ranar Lahadi, yayin buga wasansu na farko tun bayan da Real Madrid ta fitar dasu daga gasar cin kofin zakarun Turai a ranar Laraba.
Sai dai Kylian Mbappe, wanda mai yiwuwa ya koma Real Madrid nan gaba kadan, bai fuskanci bacin ran masu kallon ba, kasancewar ya taka rawar gani wajen cin kwallaye a dukkanin karawar da suka yi da jagororin na gasar La Liga ta Spain.
Daga karshe dai kungiyar PSG ta samu nasara kan Bordeaux da kwallaye 3-0, wadanda Mbappe da Neymar da Paredes suka jefa.
A halin yanzu kungiyar ke kan gaba a gasar Ligue 1 da maki 65, tazarar maki 15 a tsakaninta da Marseille, waddake matsayi na 2.