Dubunnan Mutane suka gudanar da zagayen jerin gwano a New York inda sukayi Allah wadarai da masu kawo matsaloli a kokarin tsayar da wuta da akeyi a Gaza.
Dubunnan mutanen sunyi zagayen ne tare da nuna goyon bayan su ga al’ummar falasdinawa, kuma sun tuke zanga zangar lumanar ne a ofishin wata kungiya da tayi kaurin suna wajen goyon bayan Isra’ila domin nuna musu rashin jin dadin su kan yadda suka bawa yunkurin samar da tsagaita wuta a Gaza matsala.
Masu zanga zangar a New York sun daga allunan sanarwa masu dauke da cewa wannan kungiya tana daukan nauyin kisan kiyashi, sa’annan suna slogan din “Free Palestine” da kuma kiran a tsagaita wuta.
Kasar amurka dai tayi beto din wani kuduri na majalisar dinkin duniya inda ta hana kokarin tsayar da yaki cikin gaggawa tsakanin Isra’ila da Gaza.
Kungiyar larabawa ne bisa jagorancin Aljeriya suka shigar da kudurin kwamirin tsaro na majalisar dinkin duniya tattare da cewa babu fatan kudurin ya samu wucewa sakamakon amurka babbar kawar Isra’ila tace ba zata goyi bayan kudurin ba kuma zata gabatar da akasin sa.
Amurka ce kurum kasar da ta ki amincewa da kudurin yayin da Ingila da ki kada kuri’a, mambobi 13 na kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya sun goyi bayan kudurin na tsayar da yakin da ya lakume fiye da rayukan mutane 29000 kamar yadda hukumomin falasdinu suka tabbatar kuma ya raba kaso 80 cikin dari na mutane da muhallan su.
See Also: Matakan Gwamnatin Tarayya Kan Tsadar Gas Din Girki
Wakiliyar amurka a majalisar dinkin duniya Linda ta musanta zargin cewa hana kudurin saboda marawa kudurin Isra’ila na kai hari ta kasa a garin Rafah ne, inda fiye da mutane miliyan 1.4 ke rayuwa.