Netanyahu ya ce Isra’ila za ta yi nasara da goyon bayansu ko kuma ba tare da goyon bayansu ba, yana mai cewa kiran da a kakabawa takunkumin makamai abin kunya ne.
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya soki shugaban Faransa Emmanuel Macron da wasu shugabannin kasashen yammacin duniya kan kiran da ake yi na dakatar da kai wa Isra’ila makamai domin amfani da shi a Gaza.
A wani taron koli da aka yi a birnin Paris ranar asabar, shugaban na Faransa ya jaddada damuwarsa kan yadda ake ci gaba da rikici a Gaza duk da kiran da aka yi na tsagaita wuta. Ya kuma soki matakin da Isra’ila ta dauka na aikewa da sojojin kasa cikin Lebanon.
Duba nan:
- Ranar tunawa da guguwar Al-Aqsa da nasarorin da aka samu
- Amurka (FBI) ta yi Gargadi kan hare-hare a ranar tunawa da guguwar Al-Aqsa
- Gaza: Netanyahu slams Macron for urging arms embargo on Israel
Mista Macron ya ce “mafi fifiko shi ne mu koma kan hanyar siyasa, mu daina kai makamai domin yaki a Gaza,” in ji BBC.
A cikin wani faifan bidiyo da ofishinsa ya fitar a ranar Lahadi, Mista Netanyahu ya ce “Kunya a gare su,” yana nufin Mista Macron da wasu shugabannin kasashen yammacin duniya da suka yi kira da a kakabawa Isra’ila takunkumin makamai.
“Yayin da Isra’ila ke yaki da sojojin dabbanci da Iran ke jagoranta, ya kamata dukkan kasashe masu wayewa su tsaya tsayin daka da bangaren Isra’ila, amma duk da haka Shugaba Macron da sauran shugabannin kasashen yamma suna kira da a kakabawa Isra’ila takunkumin makamai. Kunya a gare su,” in ji Mista Netanyahu.
“Yayin da Isra’ila ke yaki da sojojin dabbanci da Iran ke jagoranta, ya kamata dukkan kasashe masu wayewa su tsaya tsayin daka da bangaren Isra’ila, amma duk da haka Shugaba Macron da sauran shugabannin kasashen yamma suna kira da a kakabawa Isra’ila takunkumin makamai. Kunya a gare su,” in ji Mista Netanyahu.
Shugaban na Faransa ya kuma ce kaucewa ta’addanci a Lebanon wani abu ne mai muhimmanci kuma “Lubanon ba zai iya zama sabuwar Gaza ba.”
Duk da kashe dubban fararen hula, Mr Netanyahu ya ce Isra’ila tana kare kanmu daga wannan danyen aiki, Isra’ila tana kare wayewar kai daga masu neman dora mana duhun zamani na tsatsauran ra’ayi. Ka tabbata, Isra’ila za ta yi yaƙi har sai an ci nasara a yaƙin – saboda mu da kuma saboda zaman lafiya da tsaro a duniya.”
Daga baya ofishin Mista Macron ya ce Faransa “amintacciyar aminiyar Isra’ila ce”, ya kara da cewa matakin da Netanyahu ya yi ya wuce gona da iri kuma ya rabu da abokantakar da ke tsakanin Faransa da Isra’ila.
Yayin da Amurka da Faransa suka yi kira da a tsagaita bude wuta a Lebanon, Mista Macron ya ce, “Na yi nadamar cewa Firayim Minista Netanyahu ya yi wani zabi, ya dauki wannan nauyi, musamman na ayyukan kasa a kasar Lebanon.”