Yayin da hasarar soji da sojojin Isra’ila wadanda suka fadada mamayarsu a zirin Gaza ke karuwa, Firayim Ministan Isra’ila Benyamin Netanyahu ya ce za su ci gaba duk da tsadar yakin, kuma za su yanke shawarar yadda za su yi, ba wai don matsin lambar kasa da kasa ba.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya habarta maku cewa: a jawabin da ya gabatar a taron mako-mako na gwamnatin kasar da aka gudanar a birnin Tel Aviv, Netanyahu ya ce game da kisan da aka yi wa wasu karin sojojin Isra’ila 14 a zirin Gaza a karshen mako: “Yakin da ke gudana ya sanya mu biyan farashi mai yawa, amma ba mu da wani zabi illa ci gaba da yakin”
Da yake bayar da hujjar cewa sojojin Isra’ila sun samu nasarar kai wani gagarumin farmaki a zirin Gaza, Netanyahu ya bayyana cewa a tattaunawarsa ta wayar tarho da shugaban Amurka Joe Biden, ya ce za su ci gaba da fafatawa har sai sun samu nasara don haka Amurka ta fahimci hakan.
Netanyahu ya yi ikirarin cewa, labarin cewa Amurka ta toge ko kuma za ta toshe matakan aikin ba gaskiya ba ne” inda ya yi amfani da kalamai masu zuwa:
“Isra’ila kasa ce mai cin gashin kanta Hukunce-hukuncen yaki da ayyukanmu ana yin su ne bisa kididdigewa, ba zan yi cikakken bayani ba. Wadannan ba za su iya zama ta hanyar matsin lamba daga waje ba. Yadda za mu yi amfani da sojojinmu yanke shawara ce mai zaman kanta, ta sojoji ce ba ta kowa ba.”
Netanyahu ya ce burinsu shi ne su rusa Hamas, su dawo da mutanen da aka yi garkuwa da su, da kuma tabbatar da cewa ‘yan Isra’ila suna zaune lafiya a kudanci da arewa.
An sanar da cewa an kashe sojojin Isra’ila 14 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata a yankin Zirin Gaza, inda sojojin Isra’ila ke kokarin fadada mamayarsu.
Source: ABNAHAUSA