Natenyahu ya yi mamakin kalaman Biden game da tsagaita wuta a gaza
Wani babban jami’in Isra’ila ya ce Natenyahu ya yi mamakin matuka game da kalaman shugaban na Amurka ya yi kan yuwuwar yarjejeniyar tsagaita bude wuta a ranar Litinin mai zuwa.
Wani babban jami’in Isra’ila ya shaidawa tashar talabijin ta ABC cewa, Firaministan Isra’ila Benyamin Natenyahu ya yi mamakin kalaman shugaban Amurka Joe Biden game da yiwuwar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a mako mai zuwa.
kudanna link din kasa don ganin ragowar labarai:👇👇
Shugaban Amurka Joe Biden a daren jiya ya bayyana fatan ganin an tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Hamas zuwa ranar litinin mako mai zuwa.
A lokacin da yake magana da manema labarai a birnin New York, Biden a yayin da yake amsa tambaya game da abubuwan da ke faruwa a Gaza: “Ina fatan za mu cimma yarjejeniyar tsagaita wuta nan da ranar litinin mako mai zuwa.”
A halin da ake ciki, jami’an Hamas ma sun bayyana rashin jin dadinsu da tattaunawar da ake yi tsakanin bangarorin.
Jami’an Isra’ila biyu da wata majiya mai tushe sun shaidawa gidan talabijin na Axios cewa, masu shiga tsakani na Qatar sun sanar da Isra’ila cewa manyan jami’an Hamas sun ji takaicin sabunta tsarin yarjejeniyar, suna masu jaddada cewa har yanzu akwai babban gibi tsakanin shawarwari da bukatunsu.