Sayyid hassan nasrullah wanda shine babban sakataren kungiyar mukawama dinnan ta hisbullah wacce take a labanon ya tabbatar da cewa jirgi na uku da na hudu na kan hanya domin kawo man fetur daga kasar jamhuriyar musulunci ta Iran domin tabbar da samun biyan bukatun labanawa da kuma saukaka rayuwa ga labanawan a yanayin da ke ciki.
An kammala duk cike ciken faifofi domin jirgi na uku wanda ke dauke man disel ya taso zuwa labanon, a cewar sayyid nasrullah ajawakin kai tsaye daya gabatar ranar litinin.
Da yake bayani danagane da sabuwar gwamanatin labanon din wacce akayi nasara kafawa bayanin tirka tirkar da ta auku, ya bayyana cewa sabuwar gwamantin tana da ikon daukar matsaya dangane da sake shigo man zuwa nan gaba.
Duk da hakan sayyid nasrullah ya jaddada cewa ”muna bukatar wani bangare na man da labanon take amfani dashi ya zama ana shigo dashi daga jamhuriyar musulunci ta Iran”.
Kungiyar hisbullar dai ta yanke shawarar fara shigo da man fetur daga jamhuriyar musulunci ta Iran ne sakamakon takunkuman tattalin arziki da amurka ta kakaba a kan kasar labanon din sakamakon musharakar da kungiyar ta hisbullah take bisa doka da amincewa a harkokin gudanarwar labanon din.
Nasrullah ya cigaba da cewa, da wasu na ganin maganar shigo da man fetur daga Iran kawai farfaganda ce domin neman farin jini amma yanzu ta tabbatar musu da gaske ne ba farfaganda bace kamar yadda suka zata.
Ya kuma cewa kuma dai wadannan mutanen sune suke fatar isra’ila ta kaima jiragen man da hisbullah din tayo oda daga Iran.
Shugaban na hisbullah ya tabbatar da cewa duk hasashen su ya zama ba dai dai ba domin a halin isra’ila ke ciki ba zata iya wannan aiki ba, kuma ma ko ta gwada hisbullah din na da karfin da zata dauki matakan kariya cikin karfin izzah, yana ishara ga rundunar soji da kungiyar take dashi wanda tasha alwashin fito dasu domin bama kasar labanon kariya a kowanne lokaci idan bukatar hakan ta taso.
Daya juyo bangaren jamhuriyar musulunci ta Iran nasrullah ya mika godiyar sa ga jami’an gwamnatin Iran bisa tsayawa kyam wajen taimakon kasar labanon a lokacin da take bukatar hakan.