Nasrullah Iran Kasa ce Mai Karfi Da Kyakkyawan Jagoranci Da Amurka Ke Shakkun Fada Mata.
Babban sakatare janar din kungiyar Hizbullah Sayyyid Hassan nasrullah ya fadi hakan ne a wata hida da gidan talabijin din Al’alam yayi da shi ind aya nuna cewa lokacin da Imam khomaini ya bar birnin Paris zuwa filin saukar jiragen sama na Tehran shekaru 43 da suka gabata ya kasance daga ciki kwanaki masu girma abin girmamawa
Ya ce iran a lokacin mulkin sarki shah ta kasance gwamnati ce dake samun goyon bayan Amurka kuma akwai masu bada shawar fiye da dubu 60 na Amurka a bangarorin daban daban amma juyin musulunci da aka yi ya kori Amurka da isara’la baki daya daga Iran.
Daga karshe ya nuna cewa Musulunci na asali shi ne wanda yake tunkarar zalunci da ta’addanci wanda shine abin da Amurka bata yarda da shi ba, kuma Amurka tana adawa da tsarin musulunci na iran ne saboda tsarin ne mai yanci da jagoranci da baya karbar zalunci,
Daga karshe yace batun Amurka ta kai wa iran hari baraza na ce kwai da kuma matsin lamba akan iran, domin iran kasa ce mai karfi da kyakkawar jagorancin don haka Amurka take tsoron afka mata da yaki, kuma bat a isa ta dakatar da iran a ci gaba da inganta shirin tan a nukiliya ba.