Nasrallah; Wadanda Suke Neman Sasantawa Da Isra’ila Sun Kunyata Tare Da Kissan Abu-Akleh.
Babban sakatarin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa yakamata shuwagabannin kasashen Larabawa wadanda suke gaggawar samar da hulda ta HKI sun ji kunya kan kissan da Yahudawan suka yiwa Shirin Abu-Akleh, yar jarida wacce sojojin yahudawan suaka kashe a Jenin a makon da ya gabata.
Tashar talajin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sayyid Hassan Nasarallah yana fadar haka a jiya Jumma’a a lokacinda yake jawabi kai tsaye a dai dai lokacinda ake yin jana’izar Shirin a birninQudus.
Sayyid Nasaralla ya kara da cewa, wani abu mai muhimmanci dangne da kissan Abu’Akelh shi ne cewa ita kirista ce, wanda ya nuna cewa su yahudawan HKI sunakissan duk wanda ya kasance Bafalasdine Musulmi ko kirista.
A jiya Jumma’a ne dubban Falasdiawa Mazata da mata musulmi da kirista da kuma abokan aikinta yan jarida suka yi rakiya wa gawar Shirin Abu Akleh zuwa ga matwancinta kusa da wata makabaratan da iyayenta suka kwanta.
READ MORE : Kasar Rasha Za ta Yanke Wutar Lantarki Da Take Bawa Kasar Finland.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro yahudawan sun yi kokarin hana jana’azin shirin ABuAkleh a jiya jumma’a don yadda kissan ya zama masu tabo babban a tarihin kasar.