Nasarallah; Siriya Bangare Ne Na Asasi A Kawancen Gwagwarmaya Kuma Zata Ci Gaba Da Zama Hakan.
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasarallah ya bukaci hadin kai da kuma tafiya tare da gwamnatin kasar Siriya don ita asasi ce a kawancen gwagwarmaya da manufofin haramtacciyar kasar Isara’ila a yankin gabas ta tsakiya.
Tashar talabijin ta Al-almanar ta kasar kungiyar ta nakalto Nasaralla yana fadar haka ne jiya, a wani jawabinda ya gabatar dangane da ciki shekaru 40 da kafa kungiyar hizbullah a kasar Lebanon a shekara 1982.
Sayyid Nasarallah ya bayyana cewa a yau ko gobe ko kuma duk wani lokaci nan gaba, idan kasar Siriya ta fada cikin barazana ko wace irice kungiyarsa ba tare da wata tababa ba a shirye take ta shiga yaki don kareta.
Har’ila yau shugaban kungiyar ta Hizbullah ya jaddada bukatar a maida huldar jakadanci tsakanin kasashen Lebanon da Siriya, musamman ganin cewa kasar Lebanon ce zata fi amfana da maida cikekken hulda da kasar.
Dangane da al-amuran cikin gida kuma, sayyid Nasarallah ya kara jaddada cewa ba wanda ya isa ya jawo kungiyarsa ta fada cikin yakin basasa ko kuma fitana ta mazhabobin addini a cikin kasar, ganin cewa akwai wadanda ake ingizasu daga kasashen waje don yin haka.